Lamuran Afirka masu daukar hankali a jarindun Jamus
April 26, 2024"Daruruwan mutane ne suka mutu a yammacin Afirka sakamakon matsanancin zafi". Wannan shi ne taken labarin da jaridar Neue Zürcher Zeitung ta wallafa bayan gargadin da masu binciken yanayi suka gabatar da ke cewar, duniya za ta kara fuskantar tsanantar yanayi a kai a kai. Kuma wannan labarin ne mab.udin sharhunan jariduun Jamus a kan abubuwan da ke daukar hankalin a nahiyarmu ta Afirka.
Jaridar ta ce, a yanzu haka dai kasar Mali tana fuskantar yanayi mai mafi zafi a wannan shekara. Yanayi na zafi tsakanin watan Maris zuwa Yuni dai ba sabon abu ba ne ga al'ummar kasar. Sai dai ba su shiryawa yanayi na matsanancin tafi zafi da aka yi a Malin a farkon wannan wata ba.
A garin Kayes da ke yammacin kasar, ma'aunin zafin ya kai digiri 48.5 a ranar 3 ga Afrilu, wanka ke zama irinsa na farko. A tarihin kasar Mali ba a taba auna irin wannan yanayin. A nahiyar Afirka dai wannan shi ne yanayion zafi mafi tsanani da aka samu a watan Afrilu.
Hotunan garin na Kayes sun nuna yadda mutane ke kokarin neman wuraren samun sauki kamar bakin koguna. A yayin da hukumomin sun shawarci mutane da su guji motsa jiki a rana, kuma su sha akalla lita daya da rabi na ruwa a duk rana, daura da rufe makarantun.
Yankin Sahel da wani yanki na kudancin Afirka ta Yamma sun fuskanci tsananin zafi na kwanaki biyar a farkon watan Afrilu. Kasashe da dama sun ba da rahoton tsananin zafi. Baya ga kasar Mali ita ma Burkina Faso ta fuskanci tsananin zafin. A kasashen biyu, har yanzu ana auna zafin da ya kai ma'aunin Celsius 30 da dare.
A Bamako babban birnin Mali, asibitin Gabriel Toure ya ba da rahoton mutuwar mutane 102 tsakanin 1 zuwa 4 ga Afrilu. A cikin shekarar da ta gabata, an sami mutuwar mutane 130 duk watan Afrilu. A cewar asibitin, kusan rabin wadanda suka mutu sun haura shekaru 60.
Wani batu da ya mamaye jaridun Jamus din a wannan makon shi ne zaben kasar Afirka ta Kudu. A sharhinta mai taken "Tsohon shugaban Afirka ta Kudu yana kalubalantar tsohuwar jam'iyyarsa ta ANC", jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta yi nazarin halin da ake ciki dangane da zaben kasa baki dayan.
Ta ce, watakila ba zai taba yiwuwa a yi takamaimai bayani kan barnar da Jacob Zuma ya yi a lokacin shugabancinsa ba. Korar ba zato ba tsammani da aka yi waa ministar kudi shekaru tara da suka gabata kadai, ya janyo matsalar tattalin arziki mafi girma, tun bayan kawo karshen mulkin wariyar launin fata. Har yanzu Afirka ta Kudu na fama da radadin salon mulkinsa, na cefenar da masana'antun gwamnati ga 'yan kasuwa masu zaman kansu da kuma yadda aminan Zuman ne suka mamaye cibiyoyin gwamnati.
An yi ta zarge-zarge marasa adadi na cin hanci da rashawa tsawon shekaru. Shekaru shida kenan da aka tilastawa Zuma yin murabus, kuma shekaru uku kenan da fara tafiyar dare zuwa gidan yari wanda ya haifar da mummunar tarzoma. Amma yanzu Jacob Zuma dan kabilar Zulu mai shekara 82, ya dawo. Yana takara a karkashin tutar sabuwar jami'iyyarsa da ya kafa mai suna MK a takaice.
Babu alamar tsufa ko ciwo. Sakamakon rashin lafiya da ake dangantawa da shi, bai yi wani zaman gidan yari na azo a gani ba. Makwanni kadan gabanin zaben 'yan majalisar dokokin kasar, tsohon shugaban kasar Afirka ta Kudu ya zama daya daga cikin manyan matsalolin jam'iyyar ANC mai mulkin kasar. An dai dade ana ganin cewa ANC din za ta iya rasa rinjaye a kasar a karon farko cikin shekaru 30. Amma yanzu ita ma tana ta samu babban mai kalubale da ya fito daga tsattsonta.
A karshe majalisar dokokin Burtaniya ta amince da dokar da za ta ba da damar korar masu neman mafaka ba bisa ka'ida ba zuwa Rwanda inji jaridar Die Tageszeitung.
Bayan kwashe watanni ana takun saka, a karshe majalisar dokokin Birtaniya ta amince da dokar da za ta ba da damar a tusa keyar masu neman mafaka zuwa kasar Rwanda. Majalisar dottijan kasar a ranar Talata ta yi watsi da kin amincewa da gyare-gyaren da kanwarta ta waklilai ta yi na baya-bayan nan.
Firayim Minista Rishi Sunak ya yi farin ciki da nasarar amincewa da wannan mataki kan 'yan gudun hijira, wadda acewarsa za ta hana 'yan ci-rani yin kasadar bin hanyar ruwa mai hatsari da sunan shiga kasar ta Ingila.