1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Larabawa za su zuba jari a Masar

Zainab Mohammed AbubakarMarch 14, 2015

Kasashen Larabawan sun yi wanna alkawarin ne, a taron tattali na yini uku da ke gudana a Sharm el Sheikh, a karkashin jagorancin shugaba Fattah al-Sisi.

https://p.dw.com/p/1Eqn2
Ägypten Egypt Economic Development Conference - al-Sisi
Hoto: Reuters/Amr Abdallah Dalsh

Kasashen Larabawan dai sun yi alkawarin zuba jarin da zai ci kimanin dalar Amurka biliyan 12 a Masar, a taron tattali farfado da tattalin Masar da shugaba Fattah al-Sisi ke zama mai masaukin baki a Sharm el Sheikh.

Ko da yake Amurka ta je taron hannu banza, sakataren harkokin waje John Kerry ya sake jaddada matsayin Washington na goyon bayan Masar, a daidai wannan mawuyacin lokaci da take kokarin tayar da komadar tattalin arzikinta.

A taron na kwanaki uku da aka bude a jiya dai, kasashen Saudi Arabiya da hadaddiyar daular larabawa da Kuwai, sun yi alkawarin zuba jarin dala biyan hudu kowannensu. Mafi yawan kudaden dai za'a gudanar da ayyuka ne da su, a yayin da tsabar kudi dala biliyan uku zai shiga babban bankin kasar ta Masar.