Rasha: Harin martani a Ukraine
December 1, 2022Talla
Ministan harkokin kasashen ketaren na Rasha Sergei Lavrov ya bayyana hakan ne, a wata hira da ya yi da manema labarai da aka nuna ta kafar talabijin din kasar. Ya kara da cewa, tashar makamashin na bayar da gudunmawa wajen karfafa sojojin Ukraine. A cewarsa, sun kai harin ne domin rage adadin fararen hular da yakin kasashen biyu ke ritsawa da su. Haka kuma Lavrov ya yi zargin cewa, kungiyar tsaro ta NATO da Amirka ma na amfani da irin wadannan dabarun yakin a baya-bayan nan.