1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Lavrov ya zargi dakarun Ukraine da aikata ta'asa

June 12, 2014

Ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov ya yi kira da gudanar da bincike kan amfani da bama-baman da aka haramta a kan 'yan tawayen Ukraine.

https://p.dw.com/p/1CHYQ
Ukraine Krise Außenminister Gespräch 17.04.2014 Genf
Hoto: Reuters

A rikicin da ake ci gaba da yi a gabacin Ukraine, Rasha ta zargi sojojin Ukraine da amfani da haramtattun makamai a kan 'yan aware. A saboda haka ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov ya yi kira da gudanar da bincike kan zargin amfani da wasu bama-bamai da duniya ta haramta amfani da su wanda aka yi a gabacin Ukraine. A kuma halin da ake ciki babban sakataren kungiyar tsaro da hadin kai a Turai Lamberto Zannier ya yi kira ga dukkan bangarorin da ke rikici a Ukraine da su tsagaita bude wuta. Sai dai kuma yayin wannan kira an samu labarin gwabza kazamin fada tsakanin sojojin gwamnati da 'yan aware masu goyon bayan Rasha a gabacin Ukraine. Akalla mutane uku aka yi wa rauni a wata musayar wuta kusa da Luhansk.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Suleiman Babayo