1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Lebanon: Sa'ad Hariri ya yi murabus

Salissou Boukari
November 4, 2017

Shugaban gwamnatin kasar Lebanon Sa'ad Hariri ya yi murabus daga mukaminsa a wannan Asabar din kamar yadda gidan talbijin na Al-Arabiya da ke da cibiya a birnin Dubai ya shaida.

https://p.dw.com/p/2n1Ox
Libanon Beirut -  Saad Hariri bei Pressekonferenz
Firaministan Labanon mai Marabus Saad HaririHoto: Reuters/M. Azakir

Cikin jawabin da ya yi, Hariri ya zargi 'yan Shi'a na kungiyar Hezbollah da kasar Iran da ke mara musu baya wajen kokarin shirya manakisa. Firaministan na Labanon wanda ya ke a kasar Saudiyya ya ce ya yi murabus din ne daga mukaminsa na firaministan Lebanon domin ya na ji a jikinsa cewa rayuwarsa na fuskantar barazana sannan ya ce kasar ta Lebanon ta koma tamkar cikin yanayin da ta samu kanta a ciki a shekara ta 2005 lokacin da aka hallaka mahaifinsa tsohon firaministan kasar Rafik Hariri wanda kuma ake zargin wasu mambobin kungiyar ta Hezbollah guda hudu da hannu a kisan da ya tayar da hankalin al'ummar kasar baki daya. Murabus din na Hariri ya bai wa kowa mamaki wanda ya zo ne shekara daya kacal bayan nadin da aka yi masa a wannan mukami.