Legas: Amfani da kwale-kwale a matsayin tasi don kauce wa cunkoso
Lokacin hada-hada abubuwa kan tsaya cak kan tutunan Legas. Don saukaka rayuwar yau da kullum ta miliyoyin masu amfani da ababen hawa, birnin Legas ya fara amfani da hanyoyin ruwa masu dinbim fa'idoji.
Cunkoso lokacin tashi aiki
Miliyoyin masu amfani da ababen hawa a Legas sun saba da tsayuwa tsawon sa'o'i cikin cunkoso lokaci zuwa da komowa daga aiki. Akasarinsu na a kullum na amfani da gadoji uku daga yankunansu zuwa tsibiran birnin da ke zama cibiyoyin kasuwancin birnin. Ba bakon abu ba ne kwashe sa'o'i uku a hanya lokacin cunkoso.
Ga sauri, ga tsada
Lucky Jacob madinkin kayan kwalisa ya rage wa kansa dauniya a wannan yammaci. Da shi da sauran matafiya suna jiran kwale-kwalen daga Victoria Island zuwa Ikorodu. A gareshi tafiya ce ta mintuna 45 maimakon awa uku na cunkoso. "Sai sau biyu a mako nakem iya biya", inji Jacob. Kwatankancin Euro uku kowace tafiya da kwale-kwale, amma sulusi in ya hau safa.
Harkar kasuwanci mai kyau da zuba jari
"Kula da kwale-kwale ya fi kula da mota tsada", inji dan kasuwa Bolaji Alaka lokacin da yake tabbatar da tsadar tafiya da jirgin ruwan. Sunan kamfaninsa Sea Coach Boat, da ke da kwale-kwale na zamani mafi sabontaka a Legas. Jiragen ruwan Alaka na zuwa wurare dabam-dabam gudu uku.
Shara na cin injuna
Ruwayen Legas sun cika da shara. Suna zama alakakai ga kananan kwale-kwale. Domin idan sharar ledoji suka shiga cikin farfela, suna iya lalata inji. Saboda haka kowane kwale-kwalen Sea Coach Boat ke da injuna guda biyu. Da haka Bolaji Alaka ke tabbatar cewa kwale-kwale na aiki ko inji daya ya tsaya. A waje kan kasa ake aikin gyaransu.
Kananan kwale-kwale marasa inganci
Sai dai ba dukkan kamfanonin kwale-kwalen na sufurin jama'a ne ke da inganci ba. Kwale-kwalen dai na da bakin suna ga daukacin 'yan Najeriya da akasarinsu ke suka game da rashin kula da ingancinsu. Sau da yawa kwale-kwalen kanana ne, sun tsufa kuma ana cika su makil da mutane. A watan Mayu wani fasinja ya mutu sannan 27 sun jikkata bayan wani karo.
Karin matakan inganta sufurin kwale-kwale
Matakan inganta sufurin kwale-kwale da tabbatar da lafiyarsu shi ne burin da gwamnatin Legas ta sa gaba yanzu. Ta ba wa wani kamfani mai zaman kanshi aikin binciken lafiyar kwale-kwalen sufurin mutane. Sakamakon bai yi kyau ba. Dole za a canja gaba ki-daya dukkan kwale-kwale bakwai na gwamnati, domin ba su cika ka'idojin da aka gindaya ba.
Cunkoso: Har yanzu ba a rabu da bukar ba
Juyin-juya halin sufuri a Legas bai tabbata ba. Domin da yawa daga cikin hanyoyin ruwan Legas ba su da zurfin da manyan jiragen ruwa za su iya bi kai. Idan ana son sufurin kwale-kwalen ya inganta ya kuma zauna da gindinsa, za a bukaci jari na miliyoyin kudi. Kafin lokacin mafi yawan 'yan Najeriya ba su da zabi, dole a kullum su bi ta kan titunan Legas masu cunkoson ababen hawa.