Fasahar alkinta bola a Legas
October 2, 2019Chukuma wanda ya fito daga gabashin Najeria yayi karatunsa a fannin fasahar zane-zane kana kuma daga bisani ya kama aikin fenti da zane.
Zuwansa birnin Legas shi ya kara bude masa ido, wanda hakan ya bashi damar samun karin sani a kan fannin amfani da abubuwan da wasu ke zubarwa a matsayin mara amfani irin su gwangwanin lemo da sauransu, shi kuma yake sarrfasu zuwa abubuwan kawatarwa yana mayar su da fasalin zane.
Ya bayyana cewar yana amfani da gwangwanaye kala daban daban. Bukatar sa shine kirkirar abu sabo daga tsoho wanda yace tulin bolar dake zube ko ina a jahar Legas ita ta fara daukar hankalin sa farkon zuwan sa jahar.
"Na je bakin teku farkon zuwana Legasa, shekaru sha biyar kenan kuma nayi matukar mamaki dana ga tarin gwangwanaye a wurin, sai nake tambayar kaina, me ya kamata nayi akan hakan? Gwangwanayen gasu nan dauke da kaloli dadan daban, ni mai zane ne kuma ina kaunar kaloli."
A dai yi kiyasin Jahar Legas na da jama'a sama da miliyan ashirin, kenan akwai tarin bola mai yawa. Gerald Chukuma yana yayyanka gwangwanayen ne zuwa kanana, kana ya mannasu a jikin katako. A lokaicin da ya fara wanann harkar a shekarar 2021, shi kadai yake aikin sa amma yanzu ya dauki hayar mutane bakwai suna yi tare.
Fasahar Gerald ta kawo canji a wurin mazauna yankin da yake. Mutane sun fara ganin muhimmancin dattin dake zageya dasu har wasu daga cikin su sun shiga sana'ar dibar gwangwanaen suna masa.