An gano Uranium din da ya bata a Libiya
March 16, 2023Talla
Kakakin rundunar sojoji masu biyayya ga Khalifa Haftar janar Khaled al-Mahjoub ne ya sanar da gano da Uranium din a tazarar kilomita biyar daga tashar da ake ajiye da su a Kudancin kasar.
Gabanin sanar da batan kwantinan daraktan hukumar ta IAEA Rafael Grossi ya bayyana abin a matsayin babban abin damuwa da ka iya haifar da matsalolin tsaro na nukiliya a kasar da yaki ya daidaita.
A shekarar 2003 ne dai tsohon shugaban kasar Libiya Mouammar Kadhafi ya amince da yin watsi da shirin kera makaman nukiliya, wanda a karkashin shirin ya amince wa masu binciken makamai shiga kasar kafin daga bisani guguwar sauyi ta hambarar da shi a shekarar 2011.