Jamus: Bukatar tsagaita wuta a Libiya
January 20, 2020Talla
Gabanin kammala taron da aka gudanar a karshen mako, mahalartansa sun amince da kaddamar da matakan samar da zaman lafiya nan take tsakanin bangarorin da ke gaba da juna a Libiyan. Kasashen Rasha da Turkiyya wadanda kowa ke da bangaren da yake marwa baya a rikicin, sun amince da bukatar zauren Majalisar Dinkin Duniya na janye taimakon sojojin da suke bayarwa.
Mai masaukin baki shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta godewa shugabannin kasashen da suka halarcin taron, bayan ta yi ganawar sirri da Firaminista Fayez al-Serraj jagoran gwamnatin da Majalisar Dinkin Duniya ta amince da ita a Libiyan kafin daga bisani da gana da janar Khalifa Haftar babban kwamandan sojan da ke rike da wasu yankuna na kasar.