1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Libiya ta fara shirin girka majalisar zartarwa

November 1, 2011

Majalisar wucin gadin Libiya ta ayyana sabon Firaminista a dai dai lokacin da NATO ta kawo ƙarshen ayyukan ta a ƙasar

https://p.dw.com/p/132fa
Shugaban majalisar wucin gadin Libiya(TNC) Mustafa Abdel JalilHoto: picture alliance/dpa

Mambobin majalisar wucin gadin ƙasar Libiya sun zaɓi Abdel Rahim Al-Kib a matsayin firaministan wucin gadi na ƙasar. Ƙwararre a harkar Ilimi daga birnin Tripoli, fadar gwamnatin ƙasar, Abdur Rahim, zai maye gurbin Mahmoud Jibril wanda ya cika alƙawarin yin murabus ɗin da dama yayi idan har aka 'yantar da Libiya daga mulkin shugaba Gadhafi. A cikin kwanaki ƙalilan masu zuwa ne ake sa ran sabon firaministan zai sanar da sunayen mambobin majalisar zartarwar ƙasar.

Ita dai majalisar wucin gadin ƙasar ta Libiya ta bayyana ƙudirin miƙa mulki ga zaɓaɓbiyar majalisar dokoki cikin tsukin watanni takwas. Majalisar ce kuma za ta samarwa ƙasar da sabon tsarin mulki, gabannin zaɓukan da jam'iyyu da dama za su shiga a dama da su a shekara ta 2013.

A wani ci gaba kuma, ƙungiyar ƙawancen tsaron NATO ta kawo ƙarshen hare-hare ta jiragen saman da ta yi tsawon watanni bakwai tana yi a ƙasar Libiya. Wannan matakin kuwa ya zo ne bayan ƙungiyar ta yi watsi da buƙatar da majalisar wucin gadin Libiya ta gabatar mata game da tsawaaita wa'adin ayyukan na ta a cikin ƙasar. A lokacin daya ke magana a birnin Tripoli, fadar gwamnatin Libiya, sakatare janar na ƙungiyar ƙawancen tsaron NATO Anders Fogh Rasmussen, ya bayyana alfaharin sa game da rawar da ƙawancen tsaron ya taka wajen kifar da gwamnatin shugaba Gadhafi:

"Ya ce, duk da cewar NATO ta kawo ƙarshen babin da ta buɗe a Libiya, amma kuma kun fara rubutawa Libiya wani sabon babi a tarihin ta. Sabuwar Libiya wadda za ta ginu bisa tafarkin 'yanci da dimoƙraɗiyya da kuma bin doka da oda, game da kare haƙƙin jama'a da kuma sasanta tsakanin al'umma. Mun san lamarin ba shi da sauƙi kuma akwai ƙalubale, amma idan kun nemi taimakon mu za mu tallafa muku."

Ko da shike NATO ta ƙaddamar da hare-haren ne cikin watan Maris a ƙarƙashin wani ƙudirin kare fararen hular da Majalisar Ɗinkin Duniya ta zartar, amma wasu na sukar ƙungiyar da laifin wuce gona da iri wajen aiwatar da tanade-tanaden ƙudirin.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Yahouza Sadissou