SiyasaAfirka
Libya: Jamus na son China da Rasha su fito da gaskiya
September 26, 2020Talla
Guenter Sautter jakadan Jamus a Majalisar Dinkin Duniya ya ce kasarsa na son kwamitin sulhu ya zauna domin yin nazari kan wannan rohoto, domin a sanar da duniya yadda wasu mutane suke kai makamai kasar Libya.
Jamus ta ce akwai bukatar a zargi wadanda ke aikata wannan barna kuma idan an kama su dumumu to ya kamata a kunyata su. To sai dai a gefe guda kasashen Rasha da China sun ci gaba da nuna adawa da matakin, inda wasu majiyoyi na sirri ke nuna yadda kasashen ke son kar a wallafa rahoton.