Likitocin Rasha biyu sun halaka a Aleppo
December 5, 2016A kasar Siriya wasu jami'an kiwon lafiya biyu 'yan kasar Rasha da suka hada da mace daya sun halaka a yayin da wani na uku ya ji munmunan rauni a cikin wasu hare-haren roka da 'yan tawaye suka kaddamar kan wani gidan assibiti na wani kauyen da ke kusa da birnin Aleppo.
Wannan hari ya zo ne a daidai lokacin da kasashen Rasha da Amirka ke shirin soma wata tattaunawa a wannan mako kan batun ficewar illahirin 'yan tawaye daga birnin Aleppo wanda a halin yanzu dakaran gwamnatin Siriyar suka kwace sama da kashi biyu daga cikin uku na unguwannin da ke a karakshin ikon 'yan tawayen.
Sai dai mayakan 'yan tawayen sun yi watsi da wannan tayi na ficewa daga birnin na biyu mafi girma a kasar ta Iraki tare da shan alwashin ci gaba da yaki har sai sun ga abin da ya ture wa buzu nadi.