1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

London ta zargi Faransa da sakaci a Calais

October 28, 2016

Birtaniya da Faransa sun samu rashin fahimta kan kulawa da ya kamata a bai wa 'yan gudun hijirar Calais da ke da karancin shekaru

https://p.dw.com/p/2Rq6Z
Frankreich Minderjährige Flüchtlinge in Calais
Hoto: picture-alliance/AP Photo/T. Camus

Wata takaddama ta kunno kai tsakanin gwamnatocin Birtaniya da Faransa kan 'yan gudun hijirar da ke da karanci shekaru da ke gararamba a sansanin Calais. Ministar cikin gidan Birtaniya Amber Rudd ta bukaci hukumomin Faransa su kare lafiyar masu karancin shekaru yadda ya kamata. Sai dai kuma takwaran aikinta na Faransa Bernard Cazeneuve ya nuna mamaki dangane da wadannan kalamai, inda ya ce dukkanin yaran na son zuwa Birtaniya ne saboda suna da dangi a kasar.

'Yan gudun hijira da ke da karancin shekaru 1451 ne Faransa ta tsugunar a cibiyoyi na wucin gadi cikin watanni biyu na baya-bayannan, yayin da Birtaniya kuma ta tari 274 a tsukin wannan lokaci. Sai dai wani mai karancin shekaru da ya fito daga Afghanistan ya ce  zai ci gaba da yunkurin shiga Birtaniya har sai hakarsa ta cimma ruwa.

" A watanni takwas da na shafe a wannan sansani, dukkanin abokai na sun shiga Birtaniya, alhali ba su da 'yan uwa a can. Ni kuwa ina da 'yan uwa a kasar. To me dalilan da za a hanani shiga kasar? Zan shiga ko ta halin kaka."