Louise Arbour ta soki Iran da taka yancin mata
March 6, 2007A yayin da ya rage kwanaki ƙalilan a gudanar da bikin ranar dunia, ta yaya mata, komishinar kulla da kare haƙƙoƙin jama´a ta MDD, Louise Arbour, da kiri taron manema labarai a birnin Geneva, na ƙasar Suizland.
Jami´ar, ta bayyana takaici, a game da yadda wasu ƙasashe, ke ci gaba da cin zarafin yaya mata.
Ta bada misali da Iran, inda a cewar ta, ranar lahadin da ta wuce, hukumomi su ka yi awan gaba, da mata fiye da 30, a lokacin da su ka shirya wata zanga-zangar lumana, gaban kotun musulunci ta ƙasa, domin neman belin wasu dangi su mata, guda 5, da halin ke cikin kurkuku.
Gwamnati na tsare da su tun ranar 8 ga watan Maris na sheakara da ta gabata.
Matan da a ka capke ranar lahadi sun shiga yajin ƙin cin abinci.
Komishina Arbour ta yi kira ga hukumomin Teheran su gaggauta sakin wannan mata.