1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyar ma'aikatan cikin jirgi sun bukaci karin albashi

Zulaiha Abubakar
December 23, 2019

Kungiyar ma'aikatan cikin jirgi, ta yi wa kamfanin  jirgin sama na Lufthansa mallakar Jamus barazanar cigaba da yajin aiki bayan an kammala hutun karshen shekara.

https://p.dw.com/p/3VFWt
Lufthansa-Flugzeug und Aufschrift mit Werbung für klimafreundliches Fliegen
Hoto: DW/A. Spaeth

Wannan jawabi na kunshe ne cikin sanarwar bayan taron da kungiyar ma'aikatan cikin jirgin ta rabawa manema labarai jim kadan bayan zaman sasantawa tsakanin kungiyar da kamfanin Lufthansa. Mataimakin shugaban kungiyar Daniel Flohr ya bayyana cewar an tashi daga zaman sasantawar baram-baram ba tare da cimma daidaito ba, a don haka shugabancin kungiyar ma'aikatan jirgin ya shirya tsaf don sanar da lokacin sabon yajin aiki. A watan Nuwamban da ya gabata ne kamfanin jiragen saman na Lufthansa ya soke wasu tafiye-tafiye sakamakon yajin aikin ma'aikatan jirgin wadanda suke bukatar karin albashi.