Lufthansa ya katse tashin jirage 290
November 6, 2015Talla
Kamfanin sufurin jiragen saman na Lufthansa mallakar kasar Jamus ya katse tashin wasu jiragen sama 290, bayan da masu aikin hidima a cikin jiragensa suka fara yajin aiki na kwanaki takwas saboda neman a biya musu wasu bukatunsu da suka shafi biyan hakkoki bayan yin ritaya.
Kamfanin dai ya tanadi dakunan otel 2,500 ga fasinjojin da za su shiga tashar Frankfurt da ke zama babbar tashar wannan jirgi a Jamus, dan kada su shiga gararamba a gari. An kuma samar da wasu gadaje kanana na wucin gadi ga dubban fasinjoji da za su dakaci jirgi na gaba a kan hanyarsu ta zuwa wasu kasashe, musamman wadanda suka fito daga kasar Indiya wadanda ba su da takardar shiga kasashen Turai. Wannan soke jirage dai za ta shafi fasinjoji 37,500.