1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Belarus ba ta taimakon Rasha a Ukraine

Lateefa Mustapha Ja'afar
March 4, 2022

Shugaban kasar Belarus Alexander Lukashenko ya musanta cewa kasarsa ta yi uwa da makarbiya wajen shiga yakin da ake yi tsakanin Rasha da Ukraine.

https://p.dw.com/p/481nY
Belarus I Shugaba Alexander Lukashenko
Shugaban kasar Belarus Alexander LukashenkoHoto: Nikolay Petrov/BelTA/AP/picture alliance

Da yake jawabi ga kafar yada labaran Belarus din, Shugaba Alexander Lukashenko ya nunar da cewa sojojin kasarsa ba su shiga cikin farmaki na musamman da Rasha take yi a Ukraine ba. Da ma dai fadar Kremlin na kiran mamayar da Moscow ta yi wa Ukraine din a matsayin farmaki na musamman, kamar yadda Lukashenko na Belarus din ya furta. A cewarsa za su kara tsaurara matakan tsaro a kan iyakar Belarus din da Ukraine, tare da yin kira ga al'ummar kasarsa kan cewa, ka da su damu babu wanda ya bukaci kasar ta shiga cikin rikicin na Rasha da Ukraine.