1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ma'aikatan filin jirgin sama a Kenya sun janye yajin aiki

Abdullahi Tanko Bala
September 11, 2024

Ma'aikatan sun gudanar da yajin aikin ne domin adawa da shirin jinginar da filin jirgin ga wani kamfanin kasar Kenya bayan da suka nuna fargabar rasa ayyukansu.

https://p.dw.com/p/4kWcj
Kenya | Filin jirgin sama na Jomo Kenyatta a birnin Nairobi
Kenya | Filin jirgin sama na Jomo Kenyatta a birnin NairobiHoto: Thomas Mukoya/REUTERS

Ma'aikatan filin jirgin sama a Kenya sun amince su koma bakin aiki bayan shafe kwana guda suna yajin aiki. Babbar kungiyar kodago ta kasar ta tabbatar da janye yajin aikin.

Sakataren hadaddiyar kungiyar kungiyar yan kwadagon Francis Atwoli ya ce gwamnati ta amince cewa shirin jinginar da filin jirgin saman ga kamfanin Adani na Indiya zai gudana ne kawai idan 'yan kungiyar kwadagon sun amince

An tabbatar wa ma'aikatan cewa babu wanda za a hukunta ko ya rasa aikinsa saboda ya shiga yajin aiki.

Ministan sufuri na kasar Kenyan Davis Chirchir ya shaida wa yan jarida cewa gwamnati za ta kare muradun yan Kenya a kokarinta na inganta filin jirgin saman zuwa na zamani.