Ma'aikatan jiya za su fara yajin aiki a Laberiya
October 12, 2014Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta bayyana cewa sama da mutane 4000 ne suka rasu ta wannan cuta, 2,300 daga wannan kasa ta Laberiya da al'ummarta ke fama da annobar Ebola.
Shugaba Ellen Johnson ta kasar ta Laberiya da ta je wata cibiyar kula da marasa lafiyar a ranar Asabar, ta yi kira ga maaikatan da su tsaya kan aikinsu a wannan lokaci da kasar ke cikin bukatarsu, a cewar mataimakin ministan lafiya Tolbert Nyenswah wanda ya ce kowa na rokon ma'aikatan da su duba irin illa da hakan zai iya haifarwa, mutane na jin jiki kuma ana samun nasara a yakin da ake.
Mambobin kungiyar ma'aikatan lafiyar ta kasa, na neman a rika basu alawus na dalar Amurka 700 a kowane wata kari kan albashinsu wanda ke tsakanin dala 200 zuwa 300. Kudin alawus din da ya zama ana bawa maaikatan saboda irin hadarin da suke fiskanta a lokacin gudanar da aikinsu baya kai wa dala 500 yanzu haka.