Ma'amala tsakanin Jamus da Indonisiya
July 10, 2012Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta gana da shugaba Susilo Bambang Yudho-Yono na Indonisiya a birnin Jakarta inda ta yadda zango.Ziyara wace ita ce ta farko da Merkel ke yi a yankin kudanci Asiya ,a ƙasar da ita ce, ta huɗu mafi yawan al'umma a duniya na zaman wata kafa ta ƙara ƙarfafa hulɗa tsakanin ƙasahen biyu.
A ganawar, shugabannin biyu, sun tattauna batutuwa da dama a ciki harda matsalar kuɗin da ake fuskanta a nahiyar Turai.Da ta ke magana da manema labarai, Merkel ta ce Indonesiya ta fahimci abin da ke faruwa a turai:
Ta ce Indonisiya ta gane halin da ake ciki, domin ita kanta a shekarun baya baya nan, ta yi fama da wahaloli, amma mu dukanin biyu mun yi imanin cewar abune dake wucewa.
Mawallafi: Abdourahman Hassane
Edita:Yahouza Sadissou Madobi