1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ba ta nemi tudun tsira a Siriya ba

Abdul-raheem Hassan
October 22, 2019

Kasashe kawayen Jamus na aza ayar tambaya kan furucin ministar tsaron kasar na cewa akwai bukatar samar da tudun mun tsira a arewacin Siriya.

https://p.dw.com/p/3Rilp
Luxemburg | Heiko Maas zur Invasion der Türkei in Syrien
Hoto: DW/B. Riegert

Ministan harkokin wajen Jamus Heiko Maas ya ce kasasashe da dama na nuna damuwa kan bukatar Jamus kan wannan mataki, sai dai ministan ya kare kasar da cewa babu wani batu mai kama da neman samar da tudun mun tsira golan a arewacin Siriya.

Shugababar jam'iyyar CDU Annegret Kramp-Karrenbauer, ta ce akwai bukatar samar da wuraren tsaro tsakanin kasashen Turkuiyya da Siriya, matakin da ya tada kura tsakanin kasashen da ke dasawa da Jamus.