1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mace-mace a wani hari a Nairobi na Kenya

April 24, 2014

Wani harin kunar bakin wake da aka aiwatar da mota da ke makare da bama-bamai ya salwantar da rayukan mutane hudu a Nairobi babban birnin kasar Kenya.

https://p.dw.com/p/1Bnes
Hoto: Reuters

Daga cikin mutane hudun da suka rasa rayukansu a birnin Nairobin dai har da 'yan sanda biyu, bayan da wata mota da aka cikata da bama-bamai ta tarwatse a gaban wani ofishin 'yan sanda. Babu dai wata kungiya da ta dauki alhakin wannan harin ya zuwa yanzu. Sai dai ma'aikatar cikin gidan Kenya ta bayyana cewa ta yi nasarar cafke wasu mutane da ake ganin cewa suna da hannu a wannan aika-aika domin yi musu tambayoyi.

Birnin na Nairobi dai ya yi kaurin suna a watannin baya-bayan nan a sigar tashin bama-bamai a inda a karshen watan da ya gabata ma dai wasu jerin hare-hare suka salwantar da rayukan mutane shida. Ita dai fadar mulki ta Nairobi ta saba dora alhakin matsalar tsaro da ta fuskanta a kan masu tsananin kishin addini na Somaliya wato 'yan al-Shabab.

Kasar Kenya ta samu kanta ciki matsalar tsaro tun bayan da gwamnatinta ta sha alwashin sa kafar wando guda da 'yan al-Shabab na Somaliya shekaru biyu zuwa uku da suka gabata.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Mohammad Nasiru Awal