Macron da Merkel za su tattauna da Rasha
June 19, 2021Talla
Jamus da Faransa sun cimma matsaya kan yadda za su yi hulda da kasashen Turkiyya da Rasha a nan gaba. Bayan wata liyafar cin abincin dare da Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi da shugaban Faransa Emmanuel Macron a birnin Berlin, ta ce tana ganin cewa Kungiyar Tarayyar Turai na fuskantar manyan matsaloli game da kasashen biyu. Amma kuma dogara da juna da sassa biyu ke yi a fannoni da dama ya sa dole su ci gaba da tattaunawa da kasashen biyu, shawarar da Shugaba Macron ya amince da ita.
Sai dai jagororin biyu sun nuna damuwa game da yiwuwar yaduwar sabon nau'in Delta na cutar corona a gasar Kwallon Kafa ta kasashen Turai musamman a Birtaniya, inda anan ma ake gudanar da wasu daga cikin wasanni.