Faransa da Birtaniya za su tunkari matsalar 'yan ci-rani
October 28, 2022Talla
Wannan na daga cikin abubuwan da shugabannin biyu suka yi magana a kai a yayin tattaunawar farko ta wayar tarho da suka yi tun bayan da Sunak ya karbi ragamar jagorancin gwamnatin Birtaniya. Kazalika Macron da Sunak sun amince sun yi tattaunawar gaba-da-gaba a wani lokaci a shekara mai zuwa.
Danganta tsakanin Faransa da Birtaniya ta yi tsami a 'yan shekarun nan, inda galibi kasashen kan nuna wa juna dan yatsa a bisa matsalolin da suka biyo bayan ficewar Birtaniya daga Kungiyar Tarayyar Turai da ma batun 'yan ci-rani da ke zirga-zirga cikin sirri ta kogin da ya hade kasashen biyu.