Scholz ya gana da Macron a Berlin
May 9, 2022Talla
Baya ga batun mamayar Rasha a Ukraine, batutuwan da za su dauki hankalin ganawar shugabannin biyu sun hada da halin da ake ciki a yankin Sahel na Afirka da alakar kasashe da yankin Balkan da manufofin EU a kan Chaina. Wannan dai shi ne karon farko da shugaban Faransan Emmanuel Macron ke ziyara a Jamus, tun bayan zabensa karo na biyu a mastayin shugaban kasa a wa'adi na biyu na tsawon shekaru biyar. Ziyarar dai na zuwa ne, a daidai lokacin da Rasha ke cika shekaru 77 da samun galaba a kan 'yan Nazi a Jamus yayin yakin duniya na biyu.