1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Macron ya tattauna da Putin da Zelensky

February 20, 2022

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron da takwaransa na Rasha Vladimir Putin sun cimma matsayar lalubo bakin zaren warware takun sakar da ke tsakanin Rasha da Ukraine.

https://p.dw.com/p/47JkD
Telefonat zwischen Macron und Putin
Hoto: Irna

Bayan kwashe tsawon sa'o'i biyu suna tattaunawa ta wayar tarho, Shugabannin biyu Macron da Putin sun amince da samar da mafita ta hanyar diflomasiyya tare da yin dukkan mai yiwuwa wajen cimma nasara. Offishin shugaba Macron na Faransa ya ruwaito cewa ana sa ran ministocin harkokin wajen kasashen biyu Faransa da Rasha za su gana a 'yan kwanaki masu zuwa.

A daya hannun kuma, shugaba Macron ya kuma tattauna da shugaba Wolodymyr Zelensky na Ukraine ta wayar tarho, kwana guda bayan da Kyiv ta ce ba za ta mayar da martana ga abin da ta kira tsokana daga Rasha ba, kana kofarta a bude take don tattaunawa da Moscow.

Tun da fari dai shugaba Zelensky ya bukaci ganawa da shugaba Putin don warware takun sakar da ke tsakaninsu, amma hakarsa ba ta cimma ruwa ba.