Macron zai jagoranci taron sauyin yanayi
December 12, 2017Talla
Taron na sauyin yanayi mai suna One Planet a Turance da kasar ta Faransa da Bankin Duniya da Majalisar Dinkin Duniya suka tsara na da nufi ne na tuni da shekaru biyu da cimma yarjejeniyar birnin Paris mai muradin rage dumama da duniya ke samu.
Taron dai na da buri ne tattaunaawa kan yadda za a zuba jari kan harkokin da suka shafi kare muhallin a matakai na yankuna da gundumomi, su kuma yi aiki tare.
Shugaba Macron dai da ke caccakar Shugaba Trump na Amirka bayan da ya bayyana ficewa daga yarjejeniyar ta Paris ya ce fitar ta Amirka ta kara musu karfin gwiwa wajen cimma burinsu inda ake samun karin kasashe da suka mara baya ga yarjejeniyar.