Taron magance matsalar sauyin yanayi
December 2, 2019An bude taron Majalisar Dinkin Duniya kan sauyin yanayi a birnin Madrid na kasar Spain, inda kimanin kasashen duniya dari biyu da ake sa ran zasu hallaci taron, ke kokarin ganin an cimma matsaya game da shawo kan barazanar da duniya ke fuskanta daga sauyin yanayi.
Ana fatan ganin, a karashen taron za a kai ga amincewa da yarjejeniyar birnin Paris na 2015, wadda ta kunshi takaita amfani da makamashin da ke gurbata iska. Gabanin soma taron dai, babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya ja hankalin duniya kan daukar kwararran matakai kan magance gurbattaciyar iskar da ake fitawar.
A baya dai an tsara gudanar da wannan taro wanda na mako biyu ne a kasar Chile amma amma aka mayar da shi kasar Spain saboda zanga-zangar da ta barke a kasar ta Chile sai dai duk da haka taron zai gudana ne karkashin jagorancin Carolina Schmidt, ministar muhallin kasar ta Chile.