Bude taro kan sauyin yanayi a Madirid
December 2, 2019Tun da fari dai an shirya za a gudanar da taron Chile ne, sai dai sakamkon rashin kammala shirin hukumomin kasar aka mayar shi zuwa Madrid babban birnin kasar Spain. Masu ruwa da tsaki kan muhallin dai, sun yaba da kokarin kasar Spain bisa daukar nauyin taron da ta yi, duk kuwa da cewa tun asali ba ita aka tsara za ta karbi bakuncinsa ba. Ministar muhalli ta Jamus Svenja Schulze ta bayyana godiyarta ga mahukuntan na Madrid, ganin cewa sun dauki nauyin taron cikin makonni hudu kacal da janye shi daga Chile. Masu zanga-zangar yaki da sauyi ko kuma dumamar yanayi a biranen kasashen duniya sun karu a bana fiye da ko wanne lokaci.
Tilas a hada hannu waje guda
Sai dai acewar Ann-Kathrin Schneider, mamba a kungiyar kare mahalli da ke kasar Jamus, duk irin wannan gangamin da ake yi a duniya zai yi tasiri ne kawai idan har shugabannin siyasa suka dauki lamarin da gaske. Shi ma dai sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya António Guterres, ya bayyanan cewa yaki da sauyin yanayi abu ne da ke bukatar hada hannun waje guda, kana kasashen duniya su nuna da gaske suke yi, kama daga kamfanoni masu zaman kansu da wakilan cibiyoyin kudi da kungiyoyin fararen hula duk su tashi tsaye kan lamarin. Babbar matsala da yaki da sauyin yanayi ke fuskanta dai ita ce yadda kamfanoni masu fitar da hayakin da ke jawo dumamar yanayi suke ta jan kafa wajen daukar matakan gaske, sai kuma uwa uba yadda kasar Amirka da ke kan gaba a fannin masana'antu a duniya ta fice daga cikin yarjejeniyar kare mahalli wacce duniya ta cimma a Paris, sakamakon adawa da kudurin wanda shugaba Donald Trump ke yi, abin da ke zama babban hadari ga daukacin shirin kare mahalli.