Kamaru: Madugun adawa ya ce da sake a zabe
November 3, 2018Talla
Dan takarar jam'iyyar adawa a Kamaru Maurice Kamto ya yi kiran a kafa kwamiti mai cin gashin kansa da zai sake kirga kuri'un zaben shugaban kasa da aka yi cikin watan jiya, aikin da musamman ya bukaci kasashen duniya su gudanar da shi. Dan takaran da alkaluman sakamakon suka bayyana shi a matsayin wanda ya zo na biyu da 14.23%, bayan Shugaba Paul Biya da ya yi nasara, ya yi kiran ne a wani faifan bidiyo da ya sake ta shafin Intanet.
Dan takaran jam'iyyar MRC wanda ya yi ikirarin lashe zaben makonni biyu kafin bayyana sakamakon, tuni gwamnatin Kamarun ta bayyana shi a matsayin wanda ya taka dokar kasa. Ya kuma yi alkawarin amincewa da duk wani sakamakon da kwamitin zai iya bayyanawa, muddin dai ba na gwamnatin Kamarun ba ne.