1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar ta karbi bakuncin Guillaume Soro

Gazali Abdou Tasawa LMJ
November 14, 2023

Muhawara ta kaure a Jamhuriyar Nijar, game da dacewa ko rashin dacewar matakin hukumomin mulkin sojan kasar na karbar Guillaume Soro tsohon madugun tawayen Cote d’Ivoire.

https://p.dw.com/p/4Ynw5
Jamhuriyar Nijar | Janaral Abdourahamane Tchiani | Juyin Mulki | Mohamed Bazoum
Jagoran gwamnatin juyin mulkin Jamhuriyar Nijar Abdourahamane TchianiHoto: ORTN/Télé Sahel/AFP/Getty Images

Tuni dai Guillaume Soro ya gana da jagoran gwamnatin juyin mulkin ta Jamhuriyar Nijar, Janar Abdourahamane Tchiani a fadarsa. Nijar din ce dai kasar Afirka ta farko da ta amince ta karbe shi, tun bayan da ya shiga wannan hali na gantali. Soro ya iso Nijar ne a kokarin da yake na kawo karshen gudun hijirarsa da batun komawarsa gida, inda bayan ganawa da shugaban mulkin sojan Nijar din ya bayyana farincikinsa.

Tuni dai wasu 'yan kasar suka soma bayyana gamsuwarsu da matakin hukumomin Nijar din da suka ce na cike da darasi na nuna jin kai, sai dai daga nashi bangaren Malam Siraji Issa shugaban kungiyar Mojen cewa ya yi matakin hukumomin zai yi illa ga kokarin da ake na kawo karshen zaman doya da manja tsakanin Nijar din da Cote D'Ivoire da ma kungiyar ECOWAS ko CEDEAO. Kawo yanzu dai babu wani cikakken bayani daga hukumomi kan ko Guillaume Soro zai nemi mafaka ne a Nijar, ko kuma zama ne na wucin gadi kafin ya samu damar komawa kasarsa.