1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dafifin mutane sun tarbi jagoran 'yan adawan Tanzaniya

Suleiman Babayo USU
January 25, 2023

Jama'a da dama sun fito domin yin maraba da jagoran 'yan adawa na kasar Tanzaniya wanda ya koma gida bayan zaman hijira a kasashen Turai.

https://p.dw.com/p/4MgKy
Tanzaniya I Tundu Lissu
Tundu Lissu jagoran 'yan adawa na TanzaniyaHoto: Eric Boniface

A wannan Laraba magoya bayan jagoran 'yan adawa na kasar Tanzaniya, Tundu Lissu, sun yi masa gagarumar tarba lokacin da ya koma gida bayan kwashe fiye da shekaru biyu yana zaman gudun hijira a kasashen Turai, yayin da aka dage takunkumin harkokin siyasa a kasar.

Jagoran 'yan adawa wanda ya kasance tsohon dan majalisar dokoki da ya yi suna wajen sukar gwamnatin.

Tundu Lissu ya bar kasar ta Tanzaniya a shekara ta 2017 bayan ruwan harsasai da ya sha inda ya tafi jinya.  A farkon wannan wata Shugaba Samia Suluhu Hassan ta kasar ta Tanzabiya ta dage takunkumin harkokin siyasa da mutumin da ta gada ya kakaba Marigayi tsohon Shugaba John Magufuli da ya rasu kan madafun iko.