Magabatan Jamus na tattauna batun 'yan gudun hijira
November 5, 2015Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta kaddamar da tattaunawa da shugabannin jam'iyya da na jihohi, dangane da mafita kan 'yan gudun hijira, a dai dai lokacin da sabbin bayanai ke nunar da cewar Jamus na shirin karbar mutane miliyan guda da ke neman mafaka.
A matsayinta na kasar da ta karfin tattalin arziki a nahiyar Turai, tsakanin Janairu zuwa Oktoba Jamus ta karbi 'yan gudun hijira dubu 758. Ma'aikatar harkokin cikin gida ta nunar da cewar, 'yan siriya ne suka fi yawa, sai mutanen da suka fito daga yankunan da ke fama da rigingimu kamar Iraki da Afganistan.
A cikin watan Oktoba kadai dai, 'yan gudun hijira dubu 181 suka mika takardar neman mafaka a nan Jamus, wanda ya dara dubu 163 na watan Satumba.
Ministan harkokin cikin gida Thomas de Maiziere, ya ki bayanai kan hasashen dubu 800 a cikin shekarar, ganin cewar masu fataucin mutane na iya fassara hakan a matsayin gayyatar mutane zuwa Jamus.