Magoya bayan Mahaman Ousmane a Nijar sun kafa kwamitin COSMO
August 4, 2015Talla
Kafa wannan komiti na COSMO ya wakana ne bayan da shugabancin jam'iyyarsa ta asali ta CDS Rahama ya kubuce masa a sakamakon kayin da abokin hamayyarsa cikin rikicin neman shugabancin jam'iyyar Alhaji Abdou Labo ya yi masa a gaban kotu.
Bikin kaddamar da wannan kwamiti na goyan bayan Mahaman Usmane ya samu halartar Shugabannin 'yan adawa da dama wadanda a gurin bikin suka sha alwashin tsayawa takara ko ana ha maza ha mata a zaben shugaban kasar mai zuwa duk da tuhume-tuhumen da suke fuskanta gaban kotu.
Tuhume-tuhuman kuma da suke zargin gwamnatin Mahamadu Issoufou da kitsa su domin haramta masu kalubalantarsa a zaben mai zuwa. Zargin da bangaren shugaban kasar ke musantawa.