1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba Issoufou ya lashe zabe a Nijar

Abdoulaye Maman Amadou/LMJMarch 23, 2016

Martani kan sakamakon zaben Nijar zagaye na byiu, da ya nunar da cewar Shugaba Mahamadou Issoufou ne ya lashe zaben.

https://p.dw.com/p/1IIII
Shugaba Mahamadou Issoufou na Jamhuriyar Nijar
Shugaba Mahamadou Issoufou na Jamhuriyar NijarHoto: DW/M. Kanta

A Jamhuriyar Nijar bayan sanar da sakamakon zagaye na biyu na zaben shugaban kasa, inda shugaba mai ci, Issoufou mahamadou ya sami nasara tare da gaggrumin rinjaye, ana ci gaba da maida martani tare da kiran tabbatar da hadin kan kasa. A jawabin da ya yi bayan da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar wato CENI ta bayyanashi a matsayin wanda ya lashe zaben, Shugaba Mahamadou Issoufou ya bukaci al'ummar kasar da su kwantar da hankula kuma su zo su hada kai domin a gudu tare a kuma tsira tare.

Kokarin cika alkawura da ya dauka wa al'ummar kasar

Ya kara da cewar zai dage tukuru domin tabbatar da ganin ya cika alkawuran da ya dauka a yakin neman zabe wajen gidan kasar baki daya tare da neman hadin kan al'umma.

Tuni dai 'yan adawar kasar suka yi watsi da sakamakon zaben da suka ayyana da cewar yana cike da da kura-kurai, inda suka zargi hukumar zaben ta CENI kuma kotun tsarin mulkin kasar da wallafa zaben da ba shi da inganci tun ma a zagayen farko, kafin ma a zo zagaye na biyu da suka kauracewa baki daya. Alhaji Mahamane Ousman tsohon shugaban kasa a Jamhuriyar ta Nijar kana jagoran 'yan adawar kasar wato COPA, ya bayyana sakamakon zabe da cewar kazantacce ne kuma ba shi da inganci, koda yake sun bukaci da a tattauna domin a gano inda kura-kuran suke da kuma hanyar da za a bi wajen gyarawa.

Alhaji Mahamane Ousman jagoran 'yan adawar kasar wato COPA
Alhaji Mahamane Ousman jagoran 'yan adawar kasar wato COPAHoto: DW/M. Kanta

Babu matsala da bangaren adawa

Bangaren da ke mulkin dai ya ce ba shi da matsala da 'yan adawa in har kan batun tattaunawar ne, ko da yake suna ganin cewar 'yan adawar sun ce ba za su sake yin magana da su ba.