Sojojin Nijar 11 sun mutu sabon hari
November 6, 2021Talla
Wata sanarwar daga ma'aikatar harkokin tsaron Nijar na zaton mayakan jihadi da suka saba kai farmaki kan iyakar Burkina Faso da Mali ne suka kaddamar da hari kan sojojin kasar da manyan makamai yayin da suka zo kan babura da motoci.
Harin ya faru ne kwanaki kalilan bayan wani mummunar harin kwantan bauna da ya yi sanadiyyar mutuwar fararen hula 69, matakin da ya sa gwamnatin Nijar ayyana makoki na kwanaki biyu.