1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mahawara kan leken asirin Amurka a Jamus

July 17, 2013

Kwamitin sa ido a kan 'yan majalisar Jamus na nazarin dangantakar dake akwai tsakanin hukumomin leken asiri na Jamus da Amurka, bisa ga musayar bayanan sirri.

https://p.dw.com/p/199qO
German Chancellor Angela Merkel attends the handover ceremony of the annual report of the National Regulatory Control Council (NKR) at the Chancellery in Berlin July 2, 2013. REUTERS/Thomas Peter (GERMANY - Tags: HEADSHOT POLITICS)
Hoto: Reuters

Kwamitin sa ido a kan 'yan majalisar Jamus ya dukufa ka'in da na'in, domin nazarin shin ko hukumar leken asirin Amurka ta shaida wa takwararta na Jamus dangane da ayyukan da take gudanarwa na lura da lamura a kasar? Kuma yunkurin kai hari nawa aka bankado a nan Jamus daga irin wadannan bayanai na sirri?

Wadannan dai su ne tambayoyin da kwamitin sa ido a kan ayyukan 'yan majalisar Jamus din ke mahawara a kai a birnin Berlin. A wannan Talatar ce dai ministan cikin gida Hans-Peter Friedrich ya bayyana a gaban jami'an kwamitin, domin bayanin ziyarar da ya kai Amurka. Ziyarar ta Friedrich a Amurka dai na da nasaba da samun bayanai daga Amurkan dangane da kwasar bayanan Jamusawa ta yanar gizo da hukumar leken asirin Amurkan ta NSA ke yi a asirce.

A yanzu haka dai babu masaniya dangane da irin abubuwan da ministan cikin gidan na Jamus ya bayyana a gaban kwamitin, kasancewar batutuwa ne da suka kunshi dukkan hukumomin tsaro da na leken asirin Jamus, kuma ganawar an yi ta cikin sirri. Alhaki ya rataya a wuyan wannan kwamiti na sa ido a kan hukumar leken asirin Jamus ta BND da na bangaren soji MAD da kare kundin tsarin mulkin kasar. Jami'ai 11 da ke kwamitin dai na wakiltar dukkan jam'iyyun dake majalisar Jamus, wadanda kuma za su ci gaba da kasancewa wakilan jama'a, bisa la'akari da ayyukan hukumomin leken asiri da dangantakarsu da gwamnati. Sai dai dukkan batutuwa da suka tattauna zai ci gaba da kasancewa sirri tsakaninsu, domin ba'a yarda 'yan majalisar su tattauna wadannan batutuwa da sauran takwarorinsu na jam'iyyarsu ko kuma a bayyane ba.

Innenminister Hans-Peter Friedrich (CSU) gibt am 05.06.2013 in Berlin eine Pressekonferenz. Er stellte die Jahresberichte des Bundesamtes für Bevölkerungsschutz und Katastrophenhilfe (BBK) und des Technischen Hilfswerks (THW) vor. Foto: Hannibal/dpa pixel
Hans-Peter FriedrichHoto: picture-alliance/dpa

Ayyukan Komitin sa ido a kan Majalisar

Hans-Christian Ströbele dan majalisa daga jam'iyyar masu fafutukar kare muhalli, ya yi tsokaci dangane da ayyukan kwamitin." Muna iya neman karin bayani daga wajen jami'an, kuma muna iya neman wasu fayal, kazalika muna iya neman karin bayanai daga Ma'aikatar Tarayya. Za mu iya daukar matakai masu yawa amma sai gwamnatin tarayya ta amince da hakan".

Wolfgang Neskovic, dake zama tsohon wakilin hukumar leken asiri ya soki yadda kwamitin ba shi da sukunin tafiyar da aikinsa kamar yadda ya kamata. A cewarsa wakilan kwamitin ba za su iya tilasta wa gwamnati ko hukumomin leken asiri ba su bayanai ba, domin ba su da wannan ikon.

Shi ma dan majalisa Hans-Christian Ströbele ya bayyana rashin gamsuwarsa dangane da bayanan siyasar gwamnatin tarayya ga kwamitin sa idon. A cewarsa akwai batutuwa masu yawa da shugabar gwamnati Angela Merkel ta sani game da kwasar bayanan Jamusawa da Amurka take yi a asirce, fiye da wadanda ta gabatar. Ya ce "yanzu ita ce shugabar gwamnati, kuma ofishinta shi ne ke shugabantar hukumar leken asiri ta tarayya".

Bukatar Merkel ta yi bayani

Rahotannin kafofin yada labaru na nuni da cewar, a 'yan shekaru da suka gabata, hukumar leken asirin Jamus ta bukaci takwararta ta NSA a Amurka, ta ajiye bayanan sadarwa a kan Jamusawa da aka sace? Ayar tambaya dai a nan ita ce, yaya za a ce hukumar ta BND ba ta da masaniya dangane da wadannan bayanai kuma ita ma gwamnati ana iya cewar ba ta da irin wannan masaniya? Steffen Bockhahn, dan majalisa ne daga jam'iyyar masu ra'ayin gurguzu.

Schleswig-Holstein/ Hans-Christian Ströbele, Bundestagsmitglied von Buendnis 90/Die Gruenen, spricht am Samstag (26.11.11) auf dem Bundesparteitag von Buendnis 90/Die Gruenen in Kiel. Im Mittelpunkt der Debatten steht die Wirtschafts- und Finanzpolitik. Foto: Markus Hibbeler/dapd
Hans-Christian StröbeleHoto: dapd

"Merkel tana da masaniya, duk da cewar za ta ce ba ta sani ba. Akwai bayanai masu yawa da muka samu daga Amurka da Birtaniya, kuma ofishin shugabar gwamnati na sane, hakan na nufin ita ma shugabar gwamnati dole tana sane".

Bayan ziyarar tasa a Amurka dai ministan cikin gida na Jamus ya yi kokarin kare leken asirin na Amurka da cewar yana bangaren yaki da ayyukan ta'addanci ne, duk da cewar ya kasa gabatar da gamsassun bayanai kan hakan.

Mawallafa: Carla Bleiker / Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Mohammad Nasiru Awal