Mai salon rawar lankwasa a Uganda
January 22, 2020Shi dai wannan yaro, ya dauki rawa wata hanyar isar da sako, da bayar da labari, a maimakon yadda wasu ke daukar rawa don nishadi kawai. Yawancin matasan da ke zuwa koyon rawa a cibiyar bada horo kan rawa, sun fito ne daga yankunan marasa galihu a babban birnin kasar ta Uganda, wato Kampala. Rawar na taimaka wa wajen saita alkiblarsu zuwa tafarkin cigaba.
Kato Katongole, ya ce:
"Ina burin zama malamin mawakan gambara wato Hip Hop na kasa da kuma kwararren mai rawar lankwasa. Kuma ina son na gina gidan da zan rika koyar da wasu mutane musamman yara har da manya. Zan rika bai wa marayu dama, da yara masu basirar rawa amma ba su da yadda za su yi, suna ta gararamba a titi. Zan taimake su ta yadda za su zama kamar ni".
Ko a gida, Kato na kwaikwayon rawar da ya ke sha'awa a gaban mahaifiyarsa, wacce ita ma ke ba shi goyon baya, tana cike da fatan rawar zai daga likkafar gidan baki daya.