1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ECOWAS za ta tattauna da Burkina Faso

Suleiman Babayo MAB
June 17, 2022

Sabon mai shiga tsakani na kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen Afirka ta Yamma ECOWAS/CEDEAO zai gana da mahukuntan Burkina Faso bisa manufofin komawa karkashin tsarin mulki.

https://p.dw.com/p/4CsQZ
Niger Symbolbild Fahne | Mahamadou Issoufou
Hoto: Boureima Hama/AFP

Mai shiga tsakani na kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen Afirka ta Yamma ECOWAS/CEDEAO, kana tsohon shugaban kasar Jamhuriyar Nijar Mahamadou Issoufou ya isa birnin Wagadugu na kasar Burkina Faso domin tattauna jadawalin tsarin mayar da kasar bisa tafarkin dimukaradiyya.

Kungiyar ta dakatar da Burkina Faso lokacin da sojoji suka kwace madafun iko tare da barazanar daukan tsauraran matakai kan kasar.

Mambobin kasashen na ECOWAS/CEDEA 15, suka nada Mahamadou Issoufou tsohon shugaban kasar ta Jamhuriyar Nijar a farko wannan wata na Yuni kan shiga tsakani da samar da hanyar warware rikicin na Burkina Faso. Yayin ziyarar mai shiga tsakanin zai gana shugaban gwamnatin mulkin sojan Burkina Faso Paul-Henri Sandaogo Damiba da kuma Firaminista Albert Ouedraogo.