Mai yiwuwa Taylor ya yi shekaru 80 a kurkuku
May 4, 2012Masu shigar da kara a shari'ar tsohon shugaban kasar Liberiya Charles Taylor, sun nemi a yanke masa hukuncin dauri na shekaru 80 a gidan kaso, bayan da a makon da ya gabata aka same shi da liafin taimakawa wajen aikata miyagun laifukan keta hakkin bil adama.
Wannan hukunci na sa wanda ake shirin yankewa ran talatin ga wannan wata na Mayu idan Allah ya kaimu, zai dauki hankalin jama'a sosai, domin ganin irin tasirin da zai yi ga sauran shugabanin da ke fuskantar shari'a, kan irin wadannan laifuka a kotun hukunta manyan laifukan yaki ta Duniya wato ICC da ke Hague. Inda ake sa ran tsohon shugaban kasar Côte d'Ivoire Laurent Gbagbo zai fuskanci shari'a dangane da laifukan da suka shafi cin zarafin bil adama.
A makon da ya gabata, masu shari'a suka sami Taylor mai shekaru 64 na haihuwa da laifin taimakawa kungiyoyin 'yan tawaye wadanda lokacin yakin basasar Saliyo suka ci zarafin fararen hula, ta hanyar kissa da yanke hannuwan da wasu gabobinsu, kana kuma suka yi amfani da kananan yara a matsayin dakarunsu,wajen aikata wannan ta'asa.
Mawallafiya: Pinado Abdu-Waba
Edita: Mohammed Awal Balarabe