Boko Haram sun lalata hanyoyin wutar lantarki
February 2, 2021Talla
Ana zargin kungiyar ISWAP mai ikrarin jihadi a yammacin Afirka da alhakin kai hari, wanda shi ne karo na uku da mayakan Boko Haram ke kaddamar da harin a jihar ta Borno ta Najeriya, jihar da yaki da masu da'awar jihadi ya daidaita.
Birnin Maiduguri da ke zama fadar gwamnatin jihar Borno inda mayakan na Boko Haram suka fi kai hare-hare, ya tsinci kanshi cikin mawuyacin hali daga mayakan tun bayan da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sanar da sauke hafsoshin tsaron kasar tare da maye gurbinsu da sabbi.