1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisa ta amince da kasafin kudi a Nijer

Mamman Kanta/ YBOctober 13, 2015

Nan gaba ne kuma za'a gabatar wa majalisar dokokin sabon kasafin kudin da gwamnati za ta yi aiki da shi a shekarar da za ta kama.

https://p.dw.com/p/1GnKk
Gebäude der Nationalversammlung in Niamey Niger
Zauren majalisar dokoki a jamhuriyar NijerHoto: DW

A jamhuriyar Nijar a yayin da take zamanta majalisar dokokin kasar domin duba tsarin kasafin kudaden kasar, a yammacin Litinin ne 'yan majalisar suka amince da gyaran fuskar tsarin kasafin kudin da aka yi aiki da shi a wannan shekarar da ke shirin karewa, wanda 'yan majalisar adawa suka yi watsi da shi.

Wannan tsarin kasafin kudin da aka yi wa gyaran fuska ya tashi kudi tsaba CFA 1.785,850 000 000. Wanda aka sami karin kudi sama da CFA 53,000 000 000. Kasfin kudin da ministan kudi da tattalin arziki Mohamed Boucha,ya ce mahimman aiyyukan da a ka yi amfani da su sun fi bada karfi wajen karkara da kiwo da noma da asibitoci da hanyoyi.

Kuskure a aiyyuka

Amma 'yan majalisar dokokin adawa da suka yi watsi da tsarin kasafin kudin sun ce akwai kura-kurai da dama cikin aiyyukan da gwamnati ta tsara da basu da ma'ana. Dan majalisa Alhaji Zanaidou Sabo,a karkashin tutar jam'iyar MNSD Nasara da ke adawa, ya bayar da misali kamar matsalar malaman makaranta na kwantiragi da kwararrun likitoci da bukatarsu ba ta taka kara ta karya a maimakon a biya musu bukatun,sai a kebe makudan kudade a dinga daukar mashawarta wadanda ba wani amfani ke garesu ba illa a taimaka wa magoya bayan siyasunsu.

Sitzung des Parlaments in Niger
Mahalarta zaman majalisa a NijerHoto: DW/M. Kanta

Dan majalisa Sabo ya tabo matsalar aiyyukan gyaran garin Maradi wato Maradi kolliya da yake cikin tangarda. Domin an rage kudaden aikin da suka kama CFA Miliyan dubu tara.Ba tare da bayar da wata kwakkwarar hujja ba.

Sai dai minista Boucha ya musanta rage kudaden aikin Maradi kolliya,wato ganin lokaci ya kure wato a watan Disamba ba za'a kammala ayukkan ba a sabowar shekarar da za ta kama za'a ci gaba da yinsu.

Niger Wahlen Politik Amadou Salifou
Amadou Salifou shugaban majalisar dokoki a NijerHoto: DW/M. Kanta