1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar Amurka na nazarin yarjejeniyar nukiliyar Iran

Zaionab Mohammed AbubakarJuly 29, 2015

Amurkan dai ta ce ba zata yi kasa a gwiwa ba wajen martanin soji, idan har bukatar hakan ta taso a kanta, duk da yarjejeniyar da aka cimma kan nukiliyar Tehran.

https://p.dw.com/p/1G79H
Barack Obama Iran Nuclear Vertrag Einigung Atom Deal
Hoto: picture-alliance/EPA/A. Harnik

Sakataren tsaron Amurka Ashton Carter ya tabbatarwa da 'yan majalisar kasar cewar, yarjejeniyar da aka cimma a kan shirin Nukiliyar Iran, tsakaninta da manyan kasashen duniya masu fada a ji, ba zai hana Amurka yin martanin karfin soji ba idan bukatar hakan ta taso.

Carter ya fada wa kwamitin kula da harkokin soji na majalisar dattijan Amurkan cewar, idan har Iran ta yi yunkurin tayar da jijiyar wuya, daura da halin da ake ciki a yankin Gabas ta Tsakiya, Amurka ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen yin martani da karfin soji.

Furucin na sakataren tsaro na zuwa ne, bayan da gwamnatin Barack Obama ta yi yunkurin gabatarwa da 'yan majalisar yarjejeniyar da aka cimma a kan shirin nukiliyar Iran a wannan wata.

Daga cikin wadanda ke bayyana a gaban kwamitin dai har da sakataren harkokin waje John Kerry da kuma na makamashi Ernest.