1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirye-shiryen zartar da kudin doka kan fursunoni

Kamaluddeen SaniNovember 10, 2015

Amirka na wani shirye-shiryen zartar da wani kudirin dokar da zata haramta dauko fursinonin dake a tsibirin Guantanamo Bay zuwa kasar Amirka.

https://p.dw.com/p/1H2aq
Guantanamo Camp 4 Symbolbild CIA Folterprogramm
Hoto: picture-alliance/ZUMA Press

A yau talatar nan ce dai majalisar dattijan Amirkan ake saran zasu kada kuri'a akan wasu kudaden kan manufofin tsaro har dala biliyan 607 wanda tuni ya samu amincewar majalisar dokokin kasar a makon da ya gabata.

Mahawarar dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da shugaba Barack Obama ke neman goyan bayan yan majalisun akan matsar da fursinonin su kimanin 112 daga tsibirin Guantanamo Bay dake a kasar Cuba zuwa Amirka.

Tun a baya ne dai majalisun ke dakile yunkurin alkawarin Shugaba Obaman tun a shekata ta 2008 lokacin da yake yakin neman kafen na cin alwashin rufe Sansanin fursunonin na dake Cuba.