1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Majalisar dattijan Amurka ta gargadi Isra'ila kan Gaza

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
December 4, 2023

Bernie Sanders ya ce wajibi ne Benjamin Netanyahu ya ba da amanna da kudurin kafin Amurka ta mika masa tallafin da yake bukata ta fuskar tsaro

https://p.dw.com/p/4ZjkE
Hoto: Bastiaan Slabbers/NurPhoto/picture alliance

'Yan majalisar dattijan Amurka da ke da kusanci da shugaba Joe Biden sun gargadi Isra'ila da ta kauce wa kai hare-hare kan fararen hula a yakin da ta ke yi a Gaza, kamar yadda aka jiyo Sanata Bernie Sanders na aika sakon ga Mr Biden.

Karin bayani:WHO na neman a kwashe mutane daga asibitin al-Shifa na Gaza

Bernie Sanders ya yi gargadin cewa wajibi ne firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ba da amanna da wannan kuduri, kafin tawagar tsaron Amurka karkashin Mr Biden ta amince da mika masa tallafin da yake bukata ta fuskar tsaro.

Karin bayani:Blinken ya kammala ziyara a Gabas ta Tsakiya da Asiya

Shugaba Biden ya mika wa majalisar dattijan Amurka bukatar amince masa domin mika tallafin dala biliyan 106 ga Ukraine da Isara'ila da ma wasu bukatu da suka shafi al'amuran tsaro, batun da ke ci gaba da janyo muhawara a majalisar.