SiyasaGabas ta Tsakiya
Majalisar Dinkin Duniya ta ce yunwa na kisa a Gaza
January 31, 2024Talla
Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, ta ce tsananin bala'in yunwa na salwantar da mutane a Zirin Gaza, sakamakon tarnaki da ake samu na shigar kayan abinci saboda jinkai.
Daraktan ayyukan agaji a hukumar lafiya ta MDD, Michael Ryan ya kuma ce yankin Falasdinu na cikin hadarin shiga mugun yanayi na fari daidai kuma lokacin da ake ci gaba da tsuke hanyoyin kai dauki wa yankin.
Isra'ila dai na i gaba da luguden wuta a Zirin Gaza, a hare-haren ramuwar gayya bayan wani kazamin hari da kungiyar Hamas ta kai Isra'ila a ranar bakwai ga watan Oktoban bara.
Akalla dai rayukan fararen hula 26 nme suka mutu a yakin ya zuwa wannan lokaci kuma galibin su mata ne da kananan yara.