SiyasaSudan
MDD ta damu da rayukan da ke salawanta a kasar Sudan
September 6, 2024Talla
Majalisar ta Dinkin Duniya, ta ce laifukan take hakkin bil Adama la-budda na wuyan gwamnati ne da kuma bangaren masu tawaye wadanda ke gaba da juna ne a Sudan din.
Daga cikin wasu laifukan da ke kan bangarorin biyu da ke rikicin a Sudan a tanadin dokokin duniya, har da cin zarafin mata da azaftarwa da kashe-kashe, wadanda duk ke laifuka ne na yaki.
Jagoran hukumar MDD a rikicin Sudan, Mohamed Chande Othman ya yi kiran da a samar da runduna mai zaman kanta da za ta kare hakkoki na fararen hula da ma kotun da za ta hukunta duk wani mai lafi da ke da alaka da kotun duniya a kasar.