1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi kan Idlib

August 30, 2018

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi ga wasu manyan kasashen da ke yaki a Siriya kan mafni da guba kan jama'a.

https://p.dw.com/p/342nA
München MSC 2018 | UN-Sondergesandter für Syrien Staffan de Mistura
Hoto: Getty Images/AFP/T. Kienzle

Majalisar Dinkin Duniya, ta yi kira ga kasashen Rasha da Iran da kuma Turkiyya, da su kiyaye duk wani yunkuri na kai hari mai muni a lardin Idlib da ke kasar Siriya, ganin yadda ayyukan soji ke tsauri a yankin.

Jakadan Majalisar ta Dinkin Duniya a Siriya, Steffan de Mistura, zai kai ziyara lardin na Idlib don ganin ba a halaka miliyoyin fararen hula da ke a wajen ba.

Rahotanni dai sun tabbatar da ganin dakarun kasashen waje masu yawa a yankin, yayin kuma da a gefe guda ake da kiyasin 'yan ta'adda akalla dubu 10.

Majalisar Dinkin Duniyar na kuma bukatar hadin kan gwamnatin Siriya, baya ga kiran kasashen uku da ta yi.

Fargabar da ake yi ita ce ta ganin ba a yi amfani da makamai masu hadari ba, musamman ma masu guba.