1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira ga kasar Girka

Zulaiha Abubakar
April 27, 2018

Hukumar da ke kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ja hankalin kasar Girka da ta kirkiri wasu cibiyoyi kan iyakar kasar da kasar Turkiyya sakamakon yawaitar 'yan gudun hijira.

https://p.dw.com/p/2wnUf
Griechenland Illegale Einwanderer in Internierungslager in Kyprinos
Hoto: picture-alliance/dpa

Hukumar ta kara da cewar cibiyoyin da ke Evros kan iyakar kasar ta Girka a halin yanzu sun yi cikar kwari sakamakon karuwar 'yan gudun hijira da adadin su yakai 2,900 daga  kasashen Siriya da Iraki a cikin wannan watan, lamarin da ya kai su amfani da ofisoshin 'yan sandan dake yankin. Har yanzu dai gwamnatin kasar Girka wacce ta jima ta na kyamar kwararar 'yan gudun hijirar cikin kasar, ba ta ce komai ba ga me da wannan  roko.