Tallafi ga Siriya bayan girgizar kasa
February 14, 2023Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniyar Antonio Guterres ne ya sanar da bukatar neman tallafin a shalkwatar majalisar da ke birnin New York na Amirka, inda ya ce kudin da za a tara za su taimaka wajen kai dauki ga rayuwar mutane kusan miliyan biyar a Siriyan na tsawon watanni uku. Ya kara da cewa, majalisar na tattauna matakin karshe na adadin kudin da za a nema domin tallafawa wadanda girgizar kasar ta rutsa da su a Turkiyya da ke makwabtaka da Siriyan. Guterres ya kuma sanar da cewa Shugaba Bashar al-Assad na Siriya ya amince da kara bude wasu kan iyakokin kasar biyu da Turkiyya, domin bai wa jami'an agaji karin damar kai dauki ga wadanda bala'in ya shafa da yawansu ya kai miliyan tara. Mummunar girgizar kassar da ta afku a makon da ya gabata a kasashen Siriya Turkiyya dai, ta yi sanadiyyar rayukan dubban mutane a Siriyan tare da kara jefa wasu miliyoyi cikin halin tasku na neman tallafin jin-kai.